YAU DA KULLUN

TAIMAMA

✍ Rubutawa: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa (Hafizahullah).

Allah ta’ala yayi umarni da yin taimama ayi sallah idan aka rasa ruwan wanka ko ruwan alwala. Acikin suratun Nisa’i da suratul Ma’idah.
Manzon Allah saw yayi taimama, kuma ya koyar da yadda ake yin taimama. Kamar yadda yazo a hadisan Ammar Bn Yasir a riwayar Bukhari Da Muslim da Ibn Majah.

Taimama shine amfani da ƙasa wajan shafawa a fuska da tafin hannu, da niyar samun damar yin sallah da sauran ibadun da ba’ayinsu sai da tsarki, saboda rashin ruwa, ko rashin lafiya da baza a iya amfani da ruwa ba saboda ita.
Abubuwan da suke jawo ayi taimama sune
Na ɗaya, rashin samun ruwa domin wanka ko alwala
Na biyu’ rashin lafiyar da zata hana amfani da ruwa
Na uku, tsoran kamuwa da rashin lafiya idan a yi amfani da ruwa
Na huɗu. rashin samun ruwan da zai isa ayi alwala ko wanka
Na biyar. idan mutum yana da ruwa amma, idan yayi amfani da shi yayi wanka ko alwala zai rasa ruwan sha.
Na shida. idan ruwa yayi tsada mutum bashi da kuɗin siya.
Na Bakwai. idan yanajin tsoran zuwa wajan neman ruwan saboda, ɓarayi sunyi kwantan ɓauna a gurin suna jiran wani yazo gurin su faɗa masa
Na takwas. idan ana halin yaƙi ko rashin zaman lafiya, kuma aka rasa ruwa
Na tara. idan aka sami rijiya babu gugan da zaa jawo ruwan
Na goma. idan aka ɗauke ruwan fanfo, kuma babu wani ruwa a kusa
Na goma sha ɗaya. idan wajan samun ruwa yayi nisa mai tsanani gashi babu abin hawa,
Na goma sha biyu idan mutum ya ji rauni kamar ƙuna ko haɗari,likita ya hana shi amfani da ruwa.
Na goma sha uku. Anayin taimama idan ana tsoran jinkirin warkewa daga ciwo sakamakon amfani da ruwa.
Duka waɗannan da makamantansu suna jawo ayi taimama ayi salla.

YADDA AKEYIN TAIMAMA

Idan za ayi taimama sai a sami guri mai tsafta, kamar ƙasa ko yashi ko birji ko dutse, da dukkan dangogin ƙasa.
Sai ayi basmala a buga hannu a gurin, sannan a karkaɗe idan wani abu ya maƙale, sai a shafa a fuska, kamar yadda mutum yake wanke fuska a lokacin da yake yin alwala, faɗin sa daga kunne zuwa ɗaya kunnen, tsawonta daga goshi zuwa haɓa. Sai ya ƙara buga hannun sa a ƙasa ya shafi tafin hannun sa zuwa maɗaurar agogo gaba da baya ciki da waje, ya cuɗa tsakanin yatsunsa. Wannan shine yadda Annabi saw ya siffantwa Ammar Bn Yasir yadda zaiyi taimama a riwayar Bukhari da Muslim. Amma sake buga hannu a kasa kafin ayi shafar hannu yazo a riwayar Ibn Majah shaikh Albani ya inganta ta. A cikin sahihu sunan abi Dauda.
Sai dai wasu malamai suna ganin a wajan shafar hannu sai an kawo har gwiwar hannu kamar yadda akeyi a wajan alwala, kamar yadda aka ruwaito daga Abdullah Ɗan Umar yana yin haka, amma riwayar Ammar tafi ƙarfi, tunda Annabi saw ya koya masa da kansa.
Idan mutum yayi taimama kafin yayi sallah sai ya sami ruwa, taimama ta ɓaci wajibi yayi alwala ko wanka kafin yayi sallah
Idan mai janaba yayi taimama yayi sallah, daga baya sai ya sami ruwa, sai yayi wanka ba tare da ya sake sallar da yayi ba.
Idan mutum yayi taimama yana cikin sallah sai ruwa ya samu, sai ya yanke sallar yayi amfani da ruwan.
Idan mutum yayi taimama yana cikin salla sai ya tuna ashe yana da ruwa, a kusa, sai ya yanke sallar, yayi amfani da ruwan.
Anayin taimama ne bayan an rasa ruwa, kuma baa cewa an rasa ruwa sai an nema, idan mutum yanajin zai iya samun ruwa kafin lokacin salla ya fita, sai ya jinkirta zuwa ƙarshen lokaci, amma kada ya bari lokaci ya fita bai yi salla ba.
Idan mutum ya farka daga bacci sai yaga yayi mafarki, gashi ana tsananin sanyi, yana tsoran idan yayi amfani da ruwa zai sami rashin lafiya, sai yayi taimama yayi salla kafin lokaci ya fita, daga baya sai yayi wanka.
Baayin taimama domin a sami jam’in salla kawai, Anayin taimama idan ana tsoran lokaci zai fita babu ruwa ko rashin lafiya ko tsoran samun larura idan anyi amfani da ruwan.

FARILLAN TAIMAMA

Farillan taimama sune farko yin niyya a lokacin da za ayi taimama, ayi niyya acikin zuciya baa faɗar niyya da baki, niyya aikin zuciya ne,
Na biyu Anayin taimama da kasa da dangoginta, ko dukkan abinda asalinsa daga ƙasa yake. Idan baa canga masa kama ba, ta hanyar ƙonawa.
Na uku Shafar fuska, faɗinta da tsawon ta kamar yadda akeyi a lokacin alwala.
Na huɗu shafar tafin hannu zuwa maɗaurar agogo ciki da baya da tsakanin yatsu.
Na biyar Jerantawa, a fara da fuska sannan ayi hannu, idan mutum ya fara da shafar hannu kafin fuska, sai ya sake shafar hannun bayan ya shafi fuska, domin a sami anyi su a jere yadda Annabi saw ya koyar.
Na shida Wajibi ayi taimama a gama a lokaci guda kada a rarraba, misali mutum ya shafi fuska sai bayan tsawon lokaci sai kuma ya shafi hannu, ko ya tashi ya tafi wani waje, sai ya shafi hannun acan.
Sunnonin taimama farawa da basmala da kuma karkaɗe hannu bayan an buga shi a ƙasa, anga wani abu ya maƙale a jikin hannun.

ABUBUWAN DA SUKE ƁATA TAIMAMA

Taimama tana ɓaci idan an sami ruwa kafin ayi sallah da taimamar.
Taimama tana ɓaci idan mara lafiya yayi ta kafin yayi amfani da ita sai ya warke, yadda zai iya amfani da ruwa babu matsala.
Taimama tana ɓaci idan mutum yayi ta sai ya tuno kafin ya fara salla ko yana cikin salla cewa yana da ruwa.
Taimama tana ɓaci,idan mutum yayi fitsari ko kashi ko fitar maziyyi ko wadiyy ko bacci mai nauyi, ko shafar mace da sha’awa, da dukkan Abubuwan da suke warware alwala.
Idan mutum yayi taimama yayi salla, bayan ya gama sallah sai ya sami ruwa, ba zai sake wannan sallar ba, sai dai yayi alwala domin sallar da zata zo a gaba.
Ba a yin taimama domin yin sallar juma’a sai idan babu ruwa, amma idan akwai ruwa wajibi ne ayi alwala ko za a rasa juma’a sai ayi azahar.
Idan ruwa yayi tsada kuma babu kuɗin da za a saya, sai ayi taimama
Idan wani yana da ruwa sai yayi maka rowar ruwan, sai kayi taimama kayi salla
Baya halatta mutum ya saci ruwa domin yayi wanka ko alwala
Baya halatta mutum ya ƙwaci ruwa domin yayi wanka ko alwala.
Amma yana iya aron ruwa yayi alwala ko wanka, yana iya rancan ruwa yayi wanka ko alwala daga baya sai ya biya.
Idan ya sami ruwan da alwala kawai zai iya, kuma gashi wanka zai yi, wasu malamai sunce yayi alwala da ruwan sai yayi taimama akan alwalar, ya haɗa taimama da alwala,
Wasu malamai suka ce yayi taimama kawai, idan akwai ƙazanta a jikin sa sai ya wanke da ruwan.
Shin ana iya yin salla biyu da taimama ɗaya? Anfiso duk sanda zaayi sallah a fara neman ruwa tukunna, idan baa samu ba sai ayi taimama, don haka wasu malamai sukayi fatawa cewa baa yin salla biyu da taimama ɗaya, kuma suka ce idan lokacin salla ya fita, taimama ta ɓaci idan zaayi salla ta gaba sai an sake taimama.
A duba Almulakkas fiqhi, alfiqu almuyassar na Shaikh Yusuf Abu Aziz, da Manyan littafan Malikiyya. Da fiqhu sunna da sahihu fiqhu sunna, da sharhohin muktasar khalil. Da sharhohin ayoyi da hadisan taimama a cikin bukhari da muslum da Sunan Abi Dauda.

Allah ya shirye mu tafarkinsa madaidaici.

1 thought on “TAIMAMA”

Leave a comment