YAU DA KULLUN

Dimbin Alkhairan Da Ke Cikin Kwanaki Goma Na Farkon Watan Zul-Hijjah

Daga Imam Murtadha Gusau

Lahadi, 02/06/2024

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Assalamu alaikum wa rahmatullah wa bara ka tuh

Ya ku bayin Allah, yau muna ranar lahadi, 25 ga watan Zul-Qa’dah, 1445 AH. Wannan ya nuna kenan, sati mai zuwa, idan Allah yasa muna cikin rayayyu, to zamu shiga cikin watan Zul-Hijjah.

Domin haka, ya kamata ku sani, cewa lallai kwanaki goma na farkon watan Zul-Hijjah, sune kwanaki mafiya daraja da falala a cikin dukkan kwanakin shekara, wadanda a cikin su ne Allah Subhanahu wa Ta’ala ya albarkaci wannan al’ummah ta Annabi Muhammad (SAW) da wasu irin muhimman damarmaki wadanda zasu zama sanadiyyar samun rahamar Allah a garesu. Su zama sanadiyyar shigarsu Aljannah, da ninninka ladarsu da daukaka darajarsu, domin rahamarsa da tausayinsa da jinkansa zuwa ga re su. Wadannan kwanaki masu matsayi ne da daraja a wurin Allah Madaukakin Sarki, shi yasa ma har yayi rantsuwa da su a cikin littafinsa mai girma. Allah Ta’ala yace:

“Ina rantsuwa da Alfijir; Da Darare goma (wato kwanaki goman farkon watan Zul-Hijjah).” [Alkur’an, 89:1-2]

Kuma Allah Ta’ala ya fada game da su, yake cewa:

“Ku ambaci Allah a cikin kwanaki sanannu (wato kwanaki goman farkon Zul-Hijjah).” [Alkur’an, 2:203]

Saboda haka ya ku ‘yan uwana Musulmi, lallai ya zama dole mu tashi tsaye, muyi kokari wurin ganin cewa mun kara Ibadun da muke yi, musamman a cikin wadannan kwanaki masu daraja na Zul-Hijjah. Manzon Allah (SAW) yace:

“Babu wasu kwanaki, wadanda ayukka na gari, ayukkan alkhairi suka fi soyuwa a wurin Allah, fiye da wadannan kwanaki goma na farkon watan Zul-Hijjah.” [Abu Dawud ne ya ruwaito]

A cikin wadannan kwanaki ana bukatar Musulmi su mayar da himma, su kara ayukkan alkhairi da ayukkan Ibadah, fiye da sauran ranaku. Kuma ana iya yin ko wane irin aiki na Ibadah a cikinsu. Amma ga kadan daga ayukkan da aka fi so Musulmi su fi mayar da hankali a kan su, kamar haka:

  1. Yawaita Zikiri, wato yawaita ambaton Allah Subhanahu wa Ta’ala.

Ambaton Allah aiki ne mai sauki kwarai da gaske, kuma aiki ne da baya da wata wahala, kuma aiki ne mai jawo wa Musulmi dimbin alkhairai masu tarin yawa, a duniyarsa da lahirarsa.

A matsayin ka na Musulmi, mai imani, ya kamata kayi kokari ka kara yawan ambaton Allah da kake yi.

Idan kana wurin aikin Hajji ne, a kasa mai tsarki, kada kayi wasa da yin talbiyyah dare da rana. Wadanda suke gida kuwa, basu samu damar zuwa aikin Hajji ba, su ma akwai bukatar su dage sosai wurin ambaton Allah da yabonsa a ko wane lokaci na cikin wadannan kwanaki goma masu daraja, masu albarka da falala mai girma.

Sannan kar a manta, akwai kabbarori na musamman da ake yi na ranakun Idi, wadanda su kan su Zikiri ne da ambaton Allah, wadanda suka hada da Tahlil, Takbir da Tahmid.

Sannan ga zikiroran da ake yi idan an gama ko wace Sallah daga cikin salloli biyar da Allah ya wajabta wa bayinsa, wato fadin Subhanallah sau 33, Alhamdulillah sau 33, da Allahu Akbar sau 34.

Sannan ga fadar Subhanallahi wa bihamdihi sau dari (100) a rana, wadanda aka ce suna kankare, suna goge, suna share dukkan zunuban mutum, komai yawansu.

Don haka bayin Allah masu girma, kun ga cewa yawaita Zikiri da ambaton Allah ba wani aiki bane mai wahala, amma sai dai dimbin falala da lada mai tarin yawa. Saboda haka bai kamata Musulmi yayi wasa ko yayi sake da wannan ba. Mu yawaita wannan aiki, musamman a cikin wadannan kwanaki goman farkon watan Zul-Hijjah, domin dacewa da garabasar da ke cikinsu.

  1. Ibadah ta biyu da ya kamata al’ummar Musulmi su kiyaye a cikin wadannan kwanaki, ita ce: yin azumin nafilah a cikin kwanaki tara na farkon wadannan kwanaki. Sunnah ce azumtar kwanaki tara na farkon wadannan kwanaki, saboda azumi yana daga cikin ayukka nagari kuma yana cikin ayukkan alkhairi.

Yazo a cikin Hadisil Kudusi, Allah Subhanahu wa Ta’ala yana cewa:

“Dukkan ayukkan dan Adam nasa ne, amma ban da azumi, shi azumi nawa ne, kuma ni kadai zan iya saka wa bawa da shi.” [Bukhari]

Sannan ya kai Dan uwa Musulmi mai girma, ka sani, har idan baka samu damar yin azumin kwana taran ba, ko ya kasance ba zaka iya yi ba, to kayi kokari kayi azumin ranar arfah, wato ranar tara ga watan Zul-Hijjah. Domin kamar yadda ka san cewa babu daren da ya kai daren Lailatul Kadri a wurin Allah, to haka ma, babu ranar da ta kai ranar arfah a wurin Allah. Manzon Allah (SAW) yana cewa:

“Babu wata rana da Allah Subhanahu wa Ta’ala yake ‘yan ta bayinsa masu yawa daga azabar wuta, kamar ranar arfah.” [Muslim ne ya ruwaito]

Kamar daren Lailatul Kadri, muyi kokari mu bata wannan rana ta arfah a wurin neman gafarar Allah, da neman rahamarsa, da kokari wurin yawaita addu’o’i da rokon Allah, domin ya yaye muna matsalolin da suke damun mu. Muyi amfani da wannan rana domin yiwa kasar mu mai albarka Najeriya addu’a da rokon Allah ya kare ta, ya taimake ta, ya magance muna dukkanin damuwowin mu.

A wannan rana ta arfah, wato tara ga watan Zul-Hijjah, Musulmin da basu samu damar zuwa aikin Hajji ba, sun samu wata irin dama ta musamman, wadda Allah Madaukakin Sarki zai yafe masu zububai na shekaru biyu, ta hanyar yin azumin wannan rana. Manzon Allah (SAW) yace:

“Yin azumin ranar arfah, zai kankare wa mutum zunubi na shekarar da ta wuce da na shekara mai zuwa.” [Muslim ne ya ruwaito]

  1. Ibadah ta uku da ya kamata mu yawaita, musamman a wadannan kwanaki goma na farkon watan Zul-Hijjah, ita ce, yawaita karatun Alkur’ani mai girma. Shi karatun Alkur’ani, kamar yadda muka sani ne, Ibadah ce daga cikin Ibadu mafiya girma, wadda ya kamata mu yawaita yi, domin samun kusanci ga Allah da kuma neman yardarsa.

Manzon Allah (SAW) yace:

“Duk wanda ya karanta harafi daya na Alkur’ani, to yana da lada cikakkiya. Kuma za’a ninninka masa wannan lada har sau goma. Annabi (SAW) yace, ba wai ina nufin Alif da Lam da Mim harafi ne ba, a’a, abinda nike nufi shine, Alif harafi ne, Lam harafi ne, Mim harafi ne.” [Tirmizi ne ya ruwaito shi]

Tsarki ya tabbata ga Allah, don Allah dubi irin dimbin lada da sakamakon da zaka samu dan uwa, idan ka karanta duk harafi daya na Alkur’ani mai girma, musamman a cikin wadannan kwanaki masu albarka, wadanda Allah Subhanahu wa Ta’ala yayi alkawarin ninninka muna lada a cikinsu. Don haka wallahi bai kamata Musulmi, wanda yasan ciwon kan sa, yayi wasa da wannan irin garabasa ko bonanza ba!

  1. Na hudu shine, mu zamanto masu yawan tuna masoyanmu, musamman wadanda suka gabata, kamar iyayen mu, da sauransu.

Da yawan mu, inda da hali, da zamu so muyi Ibadar aikin Hajji, musamman da sunan masoyan mu da Allah yayiwa rasuwa. Ko kuma idan har mun samu damar zuwa aikin Hajji, muyi masu addu’a, mu roki Allah Subhanahu wa Ta’ala ya gafarta masu, ya yafe zunubansu, yayi masu rahama, yayi masu sakamako da Aljannah Firdausi.

Ya kai Dan uwa mai girma, ya ke ‘yar uwa mai girma, idan har baku samu damar yin wannan ba, to kuna iya assasa wata sadaka mai gudana (wato sadakatul jariyyah) da sunansu, musamman a cikin wadannan kwanaki goma na farkon watan Zul-Hijjah.

Annabi Muhammad (SAW) yace:

“Idan mutum ya mutu, dukkanin ayukkansa zasu yanke, amma ban da guda uku: Sadaka mai gudana (sadakatul jariyah), ko ilimi wanda ake amfana da shi, ko da nagari, wanda yake yi masa addu’a.” [Muslim ne ya ruwaito]

Kuma Annabi Muhammad (SAW) ya fada muna cewa, bayar da ruwan sha yana daga cikin manya manyan sadakoki. Don haka samar da ruwan sha, ta hanyar gina bohol (burtsatse) ko gina rijiya da sunan wani masoyinka, zai taimaki al’ummah kwarai da gaske, kuma zai samar wa da masoyin naka hanyar samun lada da sakamako mai tarin yawa, wanda yake samunsa a cikin kabarinsa har illa masha Allah.

  1. Yawaita sallolin dare, yana daga cikin ayukkan da ya kamata Musulmi ya yawaita yi idan yana so ya samu daukaka a duniya da lahira, musamman a cikin wadannan kwanaki goma na farkon watan Zul-Hijjah.

An dauki kwanaki masu yawa a halin yanzu rabon mu da watan Ramadan, wanda a cikinsa ne muka dage da yin kokari, wurin yin aikin Ibadah domin neman daren Lailatul Kadri. Amma tun da watan Ramadan ya wuce, sai wasun mu suka yi sanyi game da yin sallolin dare. Shin amma muna da masaniyar cewa, yin sallar dare a wadannan kwanaki goman farkon watan Zul-Hijjah, daidai yake da yin sallar dare domin neman daren Lailatul Kadri?

  1. Yawaita sadaka na daga cikin ayukkan da ake bukatar Musulmi su yawaita yi, musamman a cikin wadannan kwanaki masu albarka, goma na farkon watan Zul-Hijjah.

Yawancin mutane, zamu ga cewa suna yawan sadaka, suna yawaita ba da kyauta da alkhairi a cikin watan Ramadan, da musamman ma, goman karshe na Ramadan, amma mun manta, ko bamu san cewa kwanaki goman farko na watan Zul-Hijjah su ma suna da daraja da falala irin na kwanaki goman karshe na Ramadan ba. Kuma bamu san irin dimbin arziki da albarka da lada mai tarin yawa da zamu samu idan munyi aiki a kwanaki goma na farkon watan Zul-Hijjah ba.

Babban Tabi’i, kuma babban malami daga cikin magabata, wato Imamu Hasan Al-Basri, Allah ya jikansa da rahama, yace:

“Ka taimaki dan uwanka Musulmi, ka yaye masa wata damuwa, ka ciyar da shi, wallahi yafi maka da kayi ta zuwa aikin Hajji ko aikin Umarah ko wace shekara.”

Taimakon ‘yan uwan mu Musulmi tare da basu tallafi, taimakon marayu da mabukata a cikin wannan al’ummah, musamman wannan lokaci da muka samu kan mu na jarabawa, lokacin tsadar abinci da talauci da yunwa, wallahi yana daga cikin ayukkan da Allah Subhanahu wa Ta’ala yafi so, kuma yafi kauna fiye da komai.

Ku taimaki bayin Allah, ku tallafa masu, ku fitar da dukiya da abinci ku ciyar, domin rahamar Allah da jinkansa da tausayinsa su sauka a gare mu, domin Allah ya taimake ku, domin Allah ya yaye muna damuwar mu baki daya.

Bayin Allah masu girma, cibiyar mu ta yada ilimin addini, cibiyar mu da ke taimakon marayu, cibiyar mu da take ayukka da gwagwarmayar ciyar da addinin Allah gaba, sama da shekaru talatin muna wannan aiki, babu dare babu rana, tana bukatar tallafin ku da agajin ku da taimakon ku, domin gudanar da ayukkan ta.

Ga wanda yayi niyyar taimakawa domin Allah, ga asusun ajiyar mu kamar haka:

  1. Access Bank: 1779691620
  2. GTBank: 0048647196

Muna godiya, Allah ya bayar da ikon taimakawa, amin.

Ku taimaka a cikin wannan wata mai albarka na kwanaki goman farko na watan Zul-Hijjah. Ku taimaka, kuma sai Allah ya taimake ku.

Ya bayin Allah, marayun mu suna bukatar abinci da ruwan sha masu tsafta da magani ko kudin sayen magani da sauransu.

  1. Yawaita tuba da neman gafarar zunuban mu yana daga cikin ayukkan da ya kamata Musulmi su mayar da himma a kan su, musamman a cikin wadannan kwanaki masu zuwa, wadanda suke cike da dimbin falala da daraja mai yawa.

Kamar yadda muka sani, aikin Hajji yana daga cikin manyan ibadu wadanda ya kamata mu aikata a matsayin mu na Musulmi, idan dai har Allah ya bamu dama, ya bamu iko. Idan har mun tafi aikin Hajjin, sai muyi amfani sa wannan dama, mu tuba, mu roki Allah gafara, mu roki Allah ya yafe muna zunuban mu, mu nemi yafiyarsa. To amma saboda halin da ake ciki, na matsin tattalin arziki da sauransu, ba kowa ne zai iya samun damar zuwa aikin Hajjin ba. To shi yasa wannan wata na Zul-Hijjah ya zama babbar kyauta daga Allah zuwa ga bayinsa, wadda zata bamu damar ko bamu samu tafiya aikin Hajji ba, to akwai yadda zamu yi mu samu irin wannan falala, mu tuba zuwa ga Allah, mu nemi gafarar zunuban mu, ko bamu samu damar zuwa kasa mai tsarki ba.

Yawaita tuba da neman gafarar Allah, ayukka ne da suke kara kusanta mu zuwa ga Mahaliccinmu, kuma suke kara tsarkake mu daga dattin zunubi. Don haka ‘yan uwana bayin Allah, lallai ya zama wajibi a gare mu mu yawaita tuba!

  1. Halartar Sallar Idi yana daga cikin manyan ayukkan Ibadah da ake gudanarwa a cikin kwanaki goma na farkon watan Zul-Hijjah.

Sallar idi tana daya daga cikin hanyoyin da aka shar’anta muna, domin mu bayyana kan mu, a matsayin mu na al’ummar Annabi Muhammad (SAW). Kuma tana daga cikin muhimman Ibadu da ya kamata ko wane Musulmi ya halarta, sai fa in da wata lalura mai karfi, wadda za ta hana shi zuwa.

Manzon Allah (SAW) tun da yake, bai taba fashin zuwa sallar idi ba, ko wace shekara sai ya tafi. Haka a bayansa, Sahabbansa ma basu taba fashin idi ba. Annabi (SAW) ya umurci kowa da kowa ya tafi zuwa sallar idi. Yace maza da mata, kowa ya fita zuwa sallar idi. Kai saboda muhimmancin halartar sallar idi a wurin Musulmi, Annabi Muhammad (SAW) yace, kai ko da mace tana cikin jinin haila, to ta tafi zuwa idi, sai dai ba zata yi sallar ba. Annabi (SAW) yace, ta tsaya a gefe, domin ta samu albarkar da ke cikin wannan fili na idi.

  1. Ibadar Layyah na daga cikin manyan Ibadu da ake gabatarwa a cikin wadannan kwanaki goma na farkon Zul-Hijjah.

Abu Talhah Allah ya kara masa yarda ya ruwaito cewa:

“Annabi (SAW) yayi Layyah, kuma yayi Layyah ga wadanda basu da iko daga al’ummarsa, wato talakawa a cikin al’ummarsa, wadanda suka shaida babu abun bautawa da gaskiya sai Allah, kuma suka shaida Annabi Muhammad (SAW), bawansa ne kuma Manzonsa ne” [Tabarani da Ahmad ne suka ruwaito]

Saboda tausayi da jinkai irin na Manzon Allah (SAW), ya kasance ko wace shekara, duk idin babbar sallah, ya kan kara dabbobi daga dabbobin da zai yanka, domin ya gabatar da ibadar Layyah, akan sa da iyalansa da marasa karfi, wato talakawa daga cikin Al’ummarsa.

Don haka ya zama wajibi ga masu iko, suyi koyi da irin wannan hali na Manzon Allah (SAW), su gabatar da Ibadar Layyah ga marasa karfi a cikin wannan al’ummah.

Marayun mu dake karkashin kulawar mu, wadanda suke a makarantun mu suna bukatar tallafin ku. Shi yasa muka gabatar maku da asusun ajiyar bankin mu a sama, domin ku taimaka muna FISABILILLAH!

Tsarki ya tabbata ga Allah, Ya ku bayin Allah, don Allah ku kalli irin wannan hali na karamci, irin na Manzon Allah (SAW). Saboda tausayi da jinkan da yake dashi ga al’ummarsa. Ace duk shekara sai yayi Layyah saboda marasa hali daga cikin al’ummarsa. Allahu Akbar! Ya Allah, ka bamu ikon yin koyi da shi, amin.

Ya kai bawan Allah, kar ka yarda kai ma a barka a baya. Yi kokari idan kana da iko, idan kana da hali, ka bayar da gudummawa da tallafi ga talakawan wannan al’ummah, musamman albarkacin wadannan kwanaki goma na farkon watan Zul-Hijjah. Kar ka bari wannan garabasa da bonanza su wuce ka. Domin baka da tabbacin cewa, shin zaka iya kaiwa shekara mai zuwa a raye?

Yi kokari ka zamanto cikin masu raya wannan ibadah ta Layyah. Yi kokari ka zamanto cikin masu raya wannan Sunnah ta Manzon Allah (SAW), ta wadata al’ummah da naman Layyah. Ku zamo masu gode wa Allah Subhanahu wa Ta’ala akan baiwa da ni’imomin da yayi maku, kar kuyi wa Allah rowa!

Yi kokari ka kasance cikin wadanda zasu wadata wannan al’ummah da abinci da naman layyah, domin yin koyi da fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW), kuma domin albarkacin wannan wata da wadannan kwanaki goma na farkon Zul-Hijjah.

Daga karshe, ‘yan uwana masu girma, ina fatan wannan sako da wadannan bayanai, zasu taimaka maku, domin kara sani da kara fahimtar matsayin wadannan kwanaki goma na farkon wannan wata na Zul-Hijjah, a wurin Allah Subhanahu wa Ta’ala da Manzonsa (SAW). Tare da fatan wadannan bayanai zasu amfani wannan al’ummah ta Annabi Muhammad (SAW).

Ina maku fatan alkhairi, tare da fatan wannan wata na Zul-Hijjah, da wadannan kwanaki goma na farkon watan, zasu riske mu cikin koshin lafiya da amincin Allah.

Ina addu’a da rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala ya yafe kura-kuren mu da zunuban mu. Allah ya kawo muna karshen matsalolin da ke damun kasar mu Najeriya baki daya, amin.

Wassalamu alaikum,

Dan uwanku, Imam Murtadha Muhammad Gusau ya rubuta, daga Okene Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samunsa a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Leave a comment